Akalla matasa mata da maza 6,500 ne a duniya ke kamuwa da cutar Kanjamau duk mako

0

Kungiyar majalisar dinkin duniya na (UNAIDS) ta bayyana cewa an sami karain sabbin mutane miliyan 1.8 da suka kamu da cutar kanjamau a duniya.

Shugaban UNAIDS Michel Sidibe ya sanar da haka a taron kasa da kasa da aka yikan cutar kanjamau a kasar Netherlands.

Sidibe ya ce an sami haka ne a dalilin rashin maida hankali wajen kawar da cutar da ‘yan siyasa ke nunawa, rashin wayar da kan mutane game da cutar da kin bin hanyoyin gujewa kamuwa da ita.

Sannan mafi yawan gwamnatocin kasashen duniya na kin samar da isassun magununar cutar tare da samar da dabarun guje wa kamuwa da cutar kamar kwaroro roba wa mutanen kasashen su.

” Bisa ga binciken da muka gudanar bayanai sun nuna cewa kashe 47 bisa 100 na karuwai da masu shan miyagun kwayoyi na cikin mutanen da suka fi kamuwa da cutar. Sannan matasa mata da maza akalla 6,500 a duniya na kamuwa da cutar kanjamau duk mako.

” Kamata ya yi gwamnatocin duniya su gane cewa hakin su ne kare kiwon lafiyar mutanen kasashen su sannan su zage damtse wajen samar da isassun magunguna, wayar dakan mutanen su da sanar dasu hanyoyi da zasu bi don kare kan su.

Share.

game da Author