Mai Shari’a Mohammed Idris na Babbar Kotun Tarayya da ke Legas, ya sa ranar 31 Ga Yuli cewa zai yanke hukuncin makomar tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Uzor Kalu.
Ana zargin Kalu da yin harkallar naira biliyan 3.2. Sauran wadanda ake zargin sa tare sun hada da kwamishinan kudi na lokacin sa, Jones Udeogu da kuma kamfanin Slok Nigeria Ltd., mallakar Kalu.
Kalu ya jawo wa Mai Shari’a wata aya mai lamba 126 da ke cikin Dokar Gabatar da Shaidu:
Dokar ta ce ana amfani da shaida ce wadda mai bada shaida ya bayyana da kan sa ido-na-ganin-ido ya gabatar a kotu.
A kan wannan dalilin ne Awa Kalu ke kalubalantar rubutacciyar shaidar da EFCC ta gabatar wa kotu cewa ba abar kamawa ko dogaro ba ce.
Ya ce shaida mai lamba D14 da kuma D1 wadda EFCC ta bayar, ta na dauke ne da sa hannun jami’in EFCC maimakon sa hannun wani jami’in banki, tunda daga banki EFCC ta ce ta samo shaidar.
A kan haka ne ya nemi Mai Shari’a ya kori karar.
Lauyan EFCC, Rotimi Jacobs ya nuna wa kotu cewa akwai fa sauran rina a kaba, domin shaidun ai ba su kenan ba.
Kan haka ne mai shari’a ya ce a ba kotu sati daya domin ta yi nazarin shaidun. Zuwa ranar 31 Ga Yuli, za ta yanke hukunci a kan wannan kiki-kakar.
Discussion about this post