RASHA 2018: ‘Yan Najeriya 75 sun sulale a kasar Rasha

0

Akalla ‘yan Najeriya 75 ne aka nema aka rasa, wadanda suka sulale, bayan kammala wasan cin kofin duniya a Rasha.

Kakakin Yada Labaran Ma’ikatar Harkokin Waje, Elias Fatile, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai cewa, mutane 230 ne aka lissafa za a dauko a jirgin Ethiopian Airline, amma 155 kadai suka kai kan su.

Ya ce a lokacin da suke kwana a kan titin kasar Rasha, jami’an ofishin jakadanci sun rika yin amfani da albashin su domin ciyar da su.

Fatile ya ce bai ga laifin su ba idan sun zabi zama can, amma fa za su fuskanci matsala domin yanayin sanyin kasar ya wuce misali.

Share.

game da Author