Ministan Shari’a kuma Antoni Janar na Tarayya, Abubakar Malami, ya rubuta wa Sufeto Janar na ‘Yan sanda wasika cewa babu wata shaidar da ta nuna akwai hannun Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki a fashi da makamin garin Offa.
Wasikar wadda ya rubuta wa Ibrahim Idris tun a ranar 22 Ga Yuli, ya ce kamata ya yi ‘yan sanda su rika yin kwakkwaran bincike kafin su yanke hukuncin makala wa mutum kamar Saraki laifi, ba tare da kwakkwaran shaidu ba.
Haka nan kuma a cikin wasikar an wanke gwamnan jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed da Shugaban Ma’aikatan sa, Yusuf Abdulwahab cewa ba su da hannu a fashin.
Mutane shida ne kacal aka ce a tuhuma a zargin hannu cikin kisan.
Alamomi sun nuna cewa Saraki ya ki zuwa ofishin ‘yan sanda ne a ranar Talata, saboda ya samu labarin aika wasikar wanke shi da Ministan Shari’a ya rubuta wa ‘yan sanda.
Idan ba a manta ba rundunar ‘Yan sanda ta gayyaci Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, da ya bayyana domin amsa tambayoyi dangane zargin alakar da ke tsakanin sa da wasu ‘yan fashin da suka yi kisa a bankin garin Offa, cikin Jihar Kwara, watanni biyu da suka gabata.
Kakakin jami’an tsaron mai suna Mosheed Jimoh ya bayayyana haka yau, a Abuja.
Jimoh yace an kama mutane 22 da ake zargi da yin fashin, wanda ya afku a ranar 5 Ga Afrilu, a garin Offa, inda aka kashe mutane 33, cikin su kuwa har da ‘yan sanda tara.
Wadanda aka kama din sun bayyana wa ‘yan sanda matukar kusancin su da Sanata Bukola Saraki.
Cikin wadanda aka kama din akwai manyan gogarman fashi biyar da suka hada da: Ayoade Akinnibosun, Ibukunle Ogunleye, Adeola Abraham, Salawudeen Azeez, Niyi Ogundiran da kuma wasu 17, wadanda suka yi fashin banki a Offa sannan suka kashe mutane 33, ciki har da ‘yan sanda 9.
An yi sanarwar gayyatar Saraki makonni uku bayan an dauke wasu da ake zargi daga Ilorin, babban birnin jihar Kwara, aka maida su Abuja domin bincike.
Tun a lokacin dama Saraki ya yi saurin yin sanarwa cewa ‘yan sanda na neman su goga masa kashin-kaji ne.
Sai dai kuma ‘yan sandan sun ce sam ba haka ba ne, kuma suka gargade shi da ya guji tsoma bakin sa a harkokin da suka shafi masu aikata munanan laifuka.
Jawabin da rundanar ‘yan sanda ta fitar a wannan lokaci ta ce wadanda ake zargin duk sun amsa cewa ‘yan bangar siyasar Bukola Saraki ne da kuma Gwamna Abdulfatah Ahmed.
A ranar da aka yi fashin dai sai da suka dira bankuna har shida a garin, da suka hada da: (i) First Bank Offa (ii) Guarantee Trust Bank Offa (iii) ECO Bank Offa (iv) Zenith Bank Offa (v) Union Bank Offa (vi) Ibolo Micro Finance Bank Offa da kuma (vii) Hedikwatar Dibijin na ‘Yan sanda da ke Offa.
Sun kwashe miliyoyin kudade, kuma suka gudu da bindigogin ‘yan sanda samfurin AK 47 har guda 21.
Sun ce Saraki ne da Gwamna Abdulfatah ke daukar nauyin su ta hanyar ba su kudade da kuma ba su makamai da motocin zirga-zirga.
An ce an samu babban gogarman ‘yan fashin mai suna Ayeode Akinnibosun na amfani da wata kartsetsiyar mota kirar LEXUS JEEP, wadda ya manna wa sunan “SARAKI”.