Sanata Ben Bruce ya bayyana cewa wasu ‘yan bindiga sun sace sanata Dino Melaye.
Sanata Bruce ya ce wasu dauke da bindiga sun sace sanata Dino Melaye. Ya rubuta haka a shafin sa na tiwita yana mai cewa ya sami wannan bayani ne daga dan uwan sanata Dino.
Idan dai ba a manta ba jiya Laraba ne aka gurfanar da Sanata Dino Melaye a Babbar Kotun Abuja da ke Gudu.
An gurfanar da shi ne bisa laifin da aka yi zargin ya aikata a ranar 24 Ga Afrilu, inda ya dirko daga cikin motar ‘yan sanda.
Mai gabatar da kara ya shaida wa Mai Shari’a Sylvanus Orji cewa Melaye ya aikata laifuka shida.
Laifukan sun hada da kokarin arcewa daga hannun ‘yan sanda, kokarin kashe kan sa da kuma lalata motor ‘yan sanda.
Ya kara da cewa Melaye ya firo da wani ruwa a cikin wata ‘yar batta inda ya yi barazanar kashe kan sa.
Dino duk ya karyata tuhumar da ake yi masa.
Mai shari’a ya bada belin sa a kan naira milyan biyar.