Buhari ya gana da sanata Shehu Sani, da sauran Sanatocin APC

0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da Sanatocin jam’iyyar APC yau a fadar gwamnati.

Sai dai a taron shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki bai halarta ba.

Shugaban masu rinjaye na majalisa Ahmed Lawan ne ya jagoranci sanatocin zuwa fadar shugaban kasa.

Cikin wadanda ake tunanin basa tare da shugaba Buhari, kamar sanata Shehu Sani da sauran sanatoci duk sun halarta.

Share.

game da Author