An gurfanar da Dino Melaye a kotun Abuja

0

A yau ne aka gurfanar da Sanata Dino Melaye a Babbar Kotun Abuja da ke Gudu.

An gurfanar da shi ne bisa laifin da aka yi zargin ya aikata a ranar 24 Ga Afrilu, inda ya dirgo daga cikin motar ‘yan sanda.

Mai gabatar da kara ya shaida wa Mai Shari’a Sylvanus Orji cewa Melaye ya aikata laifuka shida.

Laifukan sun hada da kokarin arcewa daga hannun ‘yan sanda, kokarin kashe kan sa da kuma lalata motar ‘yan sanda.

Ya kara da cewa Melaye ya fito da wani ruwa inda ya yi barazanar kashe kan sa.

Dino duk ya karyata tuhumar da ake yi masa.

Mai shari’a ya bada belin sa a kan naira miliyan biyar.

A watan Afirilu ne Dino Melaye ya sayi tsautsayi da kudin sa, yayin da jami’an tsaro suka dauke shi zuwa Lokoja domin a kai shi can ya amsa tambayoyin zargin a ake yi masa.

Tun kafin a yi nisa, ba a kai ga fita cikin Abuja ba, Dino ya diro daga cikin motar ‘yan sandan da ke dauke da shi, ya fado kasa.

Ganau wanda ya ga sanatan zaune a kasa wasu jamai’an tsaro da matasa sun kewaye shi, a unguwar Area 1, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa wasu matasa ne suka ciccibi Sanatan suka saka shi a wata mota kirar Hilux, suka garzaya da shi asibitin Zankli, da ke Mabushi, Abuja.

Share.

game da Author