An nada Stella Ankam daya daga cikin manyan alkalan Babbar Kotun Afrika

0

An nada Stella Ankam daya daga cikin manyan alkalan Babbar Kotun Kararrakin Take Hakkin Dan Adam ta Afrika, duk kuwa da cewa akwai binciken da ke a gaban ‘yan sandan Najeriya cewa ana zargin hannun ta cikin wata mummunar harkalla ta makudan miliyoyin kudade.

An zargi Stella da laifin karkatar da shari’ar da aka zargi wasu manyan jami’an kamfanin Zinox.

Bisa wannan sakala-sakala ce har wanda ya shigar da kara ya zargi Stella da hada baki da ‘yan sanda suka rika yin walagigi da shari’ar, yi masa walle-walle da kuma je-ka-ka-dawo na tsawon lokaci.

Mai kara, Benjamin Joseph, shi ne shugaban kamfanin Citadel Oracle Concept Ltd., da ke Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Ya nemi a fitar masa da hakkin naira bilyan daya a kan su Stella da kuma jami’an Zinox.

Ya ce tun lokacin da ya shigar da korafin kan Zinox, bayan ‘yan sandan binciken kwakwaf sun gano takaddamar rikita-rikitar da aka yi wa Benjamin, sun nemi ofishin ‘yan sanda su fito da fayil din da batun rikicin yake.

Benjamin ya zargi Stella da hada baki da Zinox da kuma ‘yan sanda suka hana fayil din, kuma tun 2014 har yau su na ta shiriritar da maganar.

Ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa har sai da ya samu tsohon Sufeto Janar na ‘Yan sanda na lokacin, Solomon Arase, amma ya ce masa ya bi sannu tunda rikicin na mu’amalar kasuwanci ne.

Daga nan Benjamin ya ce ya cika da mamaki kuma fargaba ya kama shi, jin an nada Stella a matsayin mamba da ta ke cikin manyan alkalan Babbar Kotun Afrika sha daya.

A karshe ya ce ba zai taba gajiyawa ba, har sai hakkin sa ya fito.

Ya sha alwashin cewa zai tura lauyan sa ya je can hedikwatar kotun inda zai gudanar da zanga-zanga kan Stella. Sannan kuma zai je wa kotun da gamsassun takardun da zai tabbatar musu da cewa Stella ‘yar cuwa-cuwa ce.n

Share.

game da Author