Yadda aka shirya tsige Saraki daki-daki sannan abin ya ci tura

0

Sanatocin da ke goyon bayan Shugaba Muhammadu Buhari, sun yi kwakkwaran shiri, kulle-kulle da kitsa tuggu da kutunguilar yadda za su tsige Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki da Mataimakin sa, Ike Ekweremadu.

Rashin nasarar wannan shiri da suka yi ne ya tabbatar da karin maganar nan da ake cewa “wanda ya riga ka kwana, to zai riga ka tashi.”

TUGGUN FARKO

Sanatocin dai kamar yadda majiyar PREMIUM TIMES ta tabbatar, sun tsara cewa a yi amfani da jami’an tsaro ta hanyar tsarewa ko kama Saraki da Ekweremadu domin a hana su halartar zaman majalisa a jiya Talata.

Sun yi haka ne kuwa domin samun tabbataccen labarin cewa sanatoci da yawa za su yi fitar farin dango daga APC a waccan rana.

An shigo da jami’an tsaro a cikin shirin, inda aka rubuta wa Saraki wasika cewa ya kai kan sa ofishin ‘yan sanda domin ya yi karin haske kan wata wasikar da suka sa ya rubuta kan zargin hannun sa a wani fashi da makami da aka yi a garin Offa na jihar Kwara.

Mukarraban Saraki sun je fita gida da sassafe aka ga motoci jibge da ‘yan sanda sun tare titin sun kuma hana shiga da fita.

Haka mataimakin sa Ekweremadu, shi kuma sai aka rubuto masa takarda daga ofishin EFCC, aka sake bijiro da batun zargin da ake masa na mallakar kadarori. Shi ma aka ce ya kai kan sa.

Amma maimakon a bar shi ya kai kan nasa, sai EFCC ta turo jami’ai aka kewaye gidan sa.

KU DAMKE SU

Shirin da aka yi tun a tsakar dare a ranar Litinin shi ne a damke Saraki a kofar gida, a lokacin da ya ke cikin kwamba din motoci.

Haka shi ma Ekweremadu a cafke shi a daidai lokacin fitowar sa daga gida. Ekweremadu ya kwanta a cikin gida, ya ki fita.

Shi kuwa Saraki da ‘yan sanda suka kewaye motocin sa a kofar gida kan titi, su na jiran ya fito su kama shi, sai kawai labari ya bulla, bayan karfe 10 na safe cewa ai ga shi can a zauren majalisa har ya hakimce kan kujerar sa.

Kafin a fara tunanin ya aka yi ya zille ya gudu, sai aka ji har ya fara lissafa sanatocin da suka canja sheka.

Wannan sanarwa da aka rika nunawa a talbijin, ta sa Majalisar Tarayya kaurewa da ihu da hayaniya da tafi, domin a lokacin su na tarayya ba su kai ga shiga zaure ba.

YADDA AKA YI WA SHIRIN KAFAR-UNGULU

An shirya cewa idan aka cafke Saraki da Ekweremadu, Sanatoci magoya bayan Buhari za su gaggauta nada sabon shugaba da mataimaki. Sannan kuma batun wanda zai karanta sunayen wadanda suka fice daga APC, bai taso ba, tunda gogarman hasalallun Saraki ba ya kan kujerar sa.

An ce shrin ya fara kwancewa yayin da masu neman tsige Saraki da majiya ta ce su Sanata Ahmed Lawan ne, suka kasa cimma matsayar wanda za a nada sabon shugaba.

TSAKANIN LAWAN KO NDUME

Wasu na so a nada Ahmed Lawan yayin da wasu kuwa sun fi karkata ga Ali Ndume.

Sai dai kuma su biyu din sun hadu da mishkila, domin daga yanki daya suka fito da Kakakin Majalisar Tarayya, Yakubu Dogara. Wato ana ganin ba zai yiwu su fito daga yanki daya ba.

An kuma samu wata matsala saboda wata majiya ta ce an ware wasu ‘yan Buhari, irin su Sanata Abdullahi Adamu a tuggun yi wa Saraki “juyin mulki”.

RUFE KOFA DA BARAWO

Majiya ta ce wadanda suka san da yunkurin tsige Saraki ne suka tsegunta masa, shi kuma ya ki kwana a gida.

An ce motocin sa da aka jera kofar gida, duk bagaras da ‘yan sanda ne kawai aka yi. Suka kewaye motoci su na zare idanu, ba su san ba kowa ciki ba.

Share.

game da Author