Gwamnatin Kaduna ta fara gini a filin gidan Hunkuyi da ta rusa

0

Gwamnatin jihar Kaduna ta fara gina dandalin wasan yara a filin sanata Suleiman Hunkuyi da ta kwace dake lamba ta 11B layin Sambo road, Unguwar Rimi Kaduna.

Idan ba a manta ba a watan Faburairun 2018 ne gwamnatin jihar Kaduna ta rusa ginin dake kan wannan fili sannan ta kwace filin kan zargin cewa Hunkuyi ya yi shekarun da dama bai biya harajin kasa da ginin ke kai ba.

Senator Suleiman Hunkuyi

Senator Suleiman Hunkuyi

A dalilin haka Sanata Hunkuyi ya shigar da kara a babbar kotun dake Kaduna inda ya bukaci kotu ta dakatar da gwamnatin kwace lasisin filin, sannan ya roki kotu ta tilasta wa gwamnti ta biya shi naira biliyan 10 ladan rusa masa ginin da ta yi.

Sai dai kuma kash, kotu tayi watsi da karar da Hunkuyi ya shigar a dalilin rashin bayyana shaidar mallakar filin ta asali da Hunkuyi bai yi ba.

Jam’in KASUPDA Nuhu Garba ya bayyana cewa gwamnatin Kaduna ta amince ta gina wajen wasn yara a wannan fili da ta kwace.

Da aka nemi ji ta bakin sanata Hunkuyi, ya ce abinda gwamnati take yi yanzu abin kunya ne da yi masa karfa-karfa a kan fiin sa.

” Wannan abu dai karfa-karfa ne aka yi mini sannan ina kira ga mutane da suyi tir da wannan abu da gwamnatin Kaduna suke yi domin idan yau nine zai iya zama gobe kai ne.”

Share.

game da Author