Karamin ministan harkokin man fetur Ibe Kachikwu ya bayyana cewa za a gama gina matatar mai na Katsina nan da shekarar 2021.
Kachikwu ya bayyana haka ne da ya ke zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa ranar Talata.
Ya ce ana gina matatar man ne a garin Mashi.
Shi dai wannan matatar mai za ta rika sarrafa gangar mai 150,000 a duk rana sannan man za a rika turo shi daga kasar Nijar ne.
” Da ma can ana kokarin binne bututun mai ne tun daga kasar Nijar har zuwa matatar mai ta Kaduna sai aka ga mai makon ayi haka kawsi nari a gina sabuwar matata a garin Mashi, jihar Katsina.
” Ita wannan matatar mai za ta dinga sarrafa man da za a rika turo wa daga kasar Nijar, ba zai shafi man Najeriya ba. Domin Kuma dama can ita man Najeriya ba iri daya take da na Nijar ba.
Attajirin dan kasuwa a harkar mai kuma mai mallakin kamfanin Blak Oil Refinery, Ibrahim Zakari ya bayyana cewa wannan aiki zai lashe har dala biliyan 2 sannan kamfaninsa kawai zata samar da kusan duka kudin domin wannan aiki.
” Ana sa ran idan har aka kammala aikin mutane akalla 2500 ‘yan Najeriya zasu sami aikin yi.