Majalisar dokokin jihar Benuwai ta tsige kakakin majalisar ta Terkimbi Ikyange.
Majalisar ta tsige Ikyange a zaman da ta yi a yau Talata kan zargin nuna halin ko in-kula akan aikin sa da nuna wariya ga wasu ‘yan majalisa.
Shugaban masu rinjaye na majalisar Audu Sule ya bayyana haka wa PREMIUM TIMES irin dabi’un shugaban majalisar ne yasa dole su tsige shi.
” A zaben da aka yi ‘yan majalisa 23 ne suka goyi baya a tsigeshi daga cikin ‘yan majaisa 30 dake zauren.
A karshe Sule ya fadi cewa tsige kakakin majalisar bashi da alaka da rashin canza shekar sa daga jam’iyyar APC zuwa PDP
” Idan wani cikin shugabanin mu ya cancanci ya shugabance mu dole za mu zauna da shi amma idan ba haka ba za mu tsige shi.”
Discussion about this post