Shugaba Muhammadu Buhari ya jaddada manufar mulkin sa wajen bin tafarkin dimokradiyya, bayar da ‘yanci da kuma barin kowa ya bi zabin da ran sa ke so.
Sannan kuma ya nanata cewa zai yi aiki tare da dukkan mambobin da suka fice na Majalisar Tarayya da na Majalisar Dattawa.
Da ya ke manana bayan wasu mambobin tarayya da na majalisar dattawa sun fice daga APC zuwa PDP, Buhari dadin da ya ji shi ne daga cikin dukkan wadanda suka fice din, babu wanda ke kullace da shi ko ya ke fushi da shi.
Shugaban ya ce shi ma bai kullaci ko daya daga cikin su ba.
“Dukkan wadanda suka fice din nan ba su da matsala da ni ko gwamnati na. Sun samu matsala ce daga jihohin su da ta danganci batun sake fitowa takara da aka hana su ko kuma basu sami tikitin takara ba”
Daga nan sai ya sha alwashin cewa fitar ta su ba za ta rage wa APC yiwuwar samun nasarar lashe zaben 2019 ba.
A karshe ya yi musu fatan alheri a cikin jam’iyyun da suka koma.
Discussion about this post