Sama da Sanatoci 40 suka je wa Ekweremadu jaje a gidan sa

0

Sama da Sanatoci 40 ne suka je jaje da jaddada mubayi’a ga Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ike Ekweremadu a gidan sa da ke rukunin gidajen ‘yan Majalisa da ke Apo, Abuja.

Sun kai wannan ziyara ce domin jajenta masa kan kewayen da jami’an EFCC da ‘yan sanda suka yi masa, har ya kasa fita zuwa majalisa a yau Talata.

Daga cikin hamshakan Sanatocin da suka kai ziyarar har da Sanata Rabi’u Kwankwaso, Ben Murray Bruce, Suleiman Adokwe, Phillip Aduda da kuma Dino Melaye.

Wakilin mu ya ci karo da cincirindon magoya bayan Ekweremadu dauke da kwalayen da aka rubuce da kalamai na goyon bayan matainakin shugaban majalisar ta dattawa.

Share.

game da Author