WATA SABUWA: Jami’an ‘yan sanda sun hana Saraki da Ekweremadu fita daga gidajen su

0

‘Yan sanda tun da sanyin safiya bayan Sallar asubahi suka hana Kakakin Majalisar Dattawa Bukola Saraki da Mataimakin sa, ike Ekweremadu fita daga gidajen su.

Rahotannin da ke yawo tun jiya da rana a Abuja sun tabbatar da cewa a yau ne ‘yan majalisar dattawa za su yi fitar-farin-dango daga APC.

Hakan kuwa na nufin kafin yammacin yau APC za ta koma jam’iyyar marasa rinjaye a majalisa kenan.

Ana ganin wannan ne dalilin hana shugabannin majalisar fita daga gida domin kada su samu sukunin halartar zaman majalisar.

Kakakin Saraki, Yusuf Olaniyonu ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa Saraki ya sa an fita da motoci waje domin ya halarci gayyatar da yan sanda suka yi masa a ofishin SARS da ke Guzape, Abuja.

“Amma ‘yan sanda tuni sun gitta motocin su kuma sun jibge jami’ai kan titin kofar gidan, sun hana kowa shiga ko fita.”

“Yanzu haka da na ke maka magana ban iya fita waje, ina ciki.”

Shi ma kakakin Ike Ekweremadu ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa ‘yan sanda sun kewaye gidan, sun hana shi fita.

“Ba na jin zai iya fita a yau idan aka yi La’akari da yawan jami’an da aka jibge a kofar gidan sai.”

Dama dai jiya ne R-APC suka ce alkalami ya bushe, ba za su yarda a sasanta ba.

Share.

game da Author