Sama da likitoci 5000 ‘yan Najeriya ke aiki a kasar Afrika ta kudu

0

Jakadan Najeriya a kasar Afrika ta kudu Gadwin Adama ya bayyana cewa akwai likitoci akalla 5000 dake aiki a asibitocin kasar Afrika ta Kudu.

Adama ya fadi haka ne a lokacin da kungiyar likitocin Najeriya dake kasar suka ziyarce shi a ofishin sa dake Johannesburg a kasar Afrika ta kudu.

Ya ce bincike ya nuna cewa adadin yawan likitoci ‘yan Najeriya dake aiki a ko asibitin gwamnati ko kuma na kudi a Kasar Afrika ta Kudu sun kai sama da 5000.

Ya ce hakan ya na nuna cewa likitocin Najeriya ne ke taimakawa fannin kiwon lafiya da tattalin arzikin kasar sannan duk da hakan abin takaici ne yadda gwamnatin kasar bata la’akari da aiyukkan da likitoci da sauran ma’aikata ‘yan Najeriya ke yi a kasar.

Ya ce a dalilin haka likitocin sun amince su taimakawa ‘yan Najeriya marasa galihu alakawa dake zaune a kasar.

” Za kuma mu hada hannu da kungiyar likitoci da sauran ma’aikatan kiwon lafiya ‘yan Najeriya dake kasar don ganin hakan ya tabbata.

A karshe Adama ya yi kira ga sauran ma’aikata ‘yan Najeriya dake kasar da su zo su hada hannu da su domin yin irin haka a kasa Najeriya.

Share.

game da Author