Jam’iyyar PDP ta fatattaki wasu daga cikin jiga-jigan ta hudu a yammacin Litinin.
Kakakin jam’iyyar PDP Kola Ologbondiyan ya sanar da haka bayan kammala taron jam’iyyar da ya gudana yau a hedikwatar ta dake Abuja.
Wadanda a ka kora sun hada da Buruji Kashamu, Bayo Adebayo, Segun Sarki da Sanimu Sodipo.
Dukkan su dai ‘ya’yan jam’iyyar PDP ne a jihar Ogun.