Yawan saduwa da juna ta hanyar jima’I nau’i ne na tabuwar hankali – Inji WHO

0

Kungiyar kula da kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta bayyana cewa mutanen dake yawan son yin jima’I a kowani lokaci nau’i ne na samun tabuwar hankali.

WHO ta bayyana cewa muddun mutum baya cin abincin da ya kamata sannan ya mai da yin jima’i rigar sawar sa wato kullum yana tare da mace to tabbas hakan zai kawo masa matsala a lafiyar sa sannan zai yi ta fadawa cikin hadarukkan kamuwa da cututtuka dabandaban.

Bayanai sun nuna cewa yin juma’i na gajiyar da mutum saboda haka domin gujewa irin hakan ya sa bayan an kammala saduwa da juna yake da kyau mace ko namiji ya/ta samu ta hutu tare da cin abincin dake gina jiki domin hakan ne zai inganta kiwon lafiyar mutum sannan ya kare ka da ga fadawa irin wannan matsala.

WHO ta ce rashin kiyaye wadannan sharudda na jefa mutum ciki irin wannan nau’i na tabuwar hankali.

A yanzu dai kungiyar WHO ta ce yawan son yin jima’I a kowani lokaci matsala ce sai dai bata da tabbacin ko illar ta kai irin ta cha-cha ko ta shaye shayen miyagun kwayoyi.

Duk da wannan bincike da WHO tayi akwai kuma ingantattun bayanai da suke nuna cewa saduwa da juna tsakanin namiji da mace na inganta lafiyar masoya.

Saduwa da zumman jima’i yakan kara wa namiji karfin mazakuta, sannan ya sawwake wa mutum matsanancin damuwa, kuma asamu barci mai nagarta.

Bayan haka kuma a kan samu kariya daga kamuwa da cututtukan dake kama zuciya, sannan yana rage kamuwa da cutar sankara da ciwon siga.

A karshe kuma akwai bayanai da suka nuna hakan na ingantawa da kara dankon zumunci a tsakanin masoya da ma’aurata.

Share.

game da Author