Dan kunar-bakin-wake ya kashe mutane a masallacin Konduga

0

Wani dan kunar-bakin-wake ya kashe mutane bakwai kuma ya ji wa wasu bakwai rauni a wani hari da ya kai masallacin Konduga, jihar Barno.

Shugaban ‘yan kungiyar tsaro na sa kai mai suna Ali Kola ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai NAN cewa an kai harin ne a wani masallaci da ke unguwar Mainari da ke Konduga.

Ya kara da cewa har zuwa yanzu ba a san yadda aka yi wanda ya kai harin ya shiga garin har kuma ya yi nasarar shiga masallacin ba.

Babban Jami’n Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Barno, Bello Dambatta ya tabbatar da faruwar lamarin.

Garin Konduga na daya daga cikin garuruwan da Boko Haram suka fi yi wa mummunan barna a jihar Barno.

Share.

game da Author