Shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa nan ba da dadewa ba zai zama shugaban masu rinjaye.
Chukwudi ya bayyana cewa akwai tabbacin canza sheka da hasalallun ‘yan jam’iyyar APC da suka rikide suka zama ‘yan jam’iyyar APC ta Hakika zasu dawo jam’iyyar su ta PDP naa da kwanki masu zuwa.
” Kaga idan har aka yi haka na zama shugaban masu rinjaye kenana domin PDP ce za ta zama jam’iyya mai rinjaye a majalisar ba APC ba.
Chukwu ya bayyana haka ne a wajen taron jam’iyyar PDP dake gunana a hedikwatar jam’iyyar a Abuja.
Idan ba’a manta ba jam’iyyar APC ta Hakika R-APC da ta balle daga APC, ta bayyana cewa kokarin da Shugaba Muhammadu Buhari da Adams Oshimhole ke yi don sasantawa kada hasalallun cikin su su fice daga jam’iyyar, ai sun makara domin alkalami ya rigaya ya bushe.
Cikin wata takarda da kakakin R-APC, Kassim Afegbua ya sa wa hannun, ya ce shugaban su Buba Galadima ya ce ba za su taba sasantawa da APC ba.
“Ai Buhari da Oshimhole sun makaro, sun yi sake har jirgin ya cira sama.
“Masu iya magana sun cewa damisa ba ta taba canja launin jikin ta.”
Haka Afegbua ya kwatanta halayyar mulkin Buhari da na jam’iyyar APC.
“Kowa ya gane su saboda sun saba yin alkawari su na karyawa. Don haka ba za mu yarda su yaudare mu ba.
“Sun ma yaudari talakawa suka yi musu alkawurra, tun a cikin 2015 amma har yanzu shiru, to ina ga mu!
“Da Buhari ya samu mulki ai mike kafa ya yi a cikin Villa, ya bari ana wulakanta mu, aka manta da mu. Sai yanzu da ya ga zabe ya zo sannan zai fito ya sake yi mana romon-kunne? To ba za mu yarda ba.”