Mai Martaba Sarkin Katsina, Abdulmumin Kabir, ya bayyana cewa an kara tono wasu gawarwaki goma a karkashin bangayen da suka fadi sakamakon mummunar ambaliyar da take faru a garin Jibiya.
Ya yi wannan bayani ne a lokacin da wata tawaga ta kai masa ziyarar ta’aziyyar marigayi Ibrahim Commase.
Ambaliyar wadda ta mamaye yankin ranar 15 Ga Yuli, ta kashe mutane 44 kuma ta lalata gidaje sama da 500.
Sarkin na Katsina ya ce an gano gawarwakin 10 ne bayan da mutane gari suka rika jin wari na tashi a karkashin bangayen gini da suka zube.
“Daga nan sai jama’a suka shaida wa Hakimin Jibiya, shi kuma ya ce a tona a zakulo su.
“Daga baya ya sanar da ni, domin mu ma a nan za mu kara rubuta sunayen mamatan a jerin sunayen wadanda ambaliyar ta kashe.”
Daga nan sai Sarki ya yi kira da cewa wadanda ibtila’in ya shafa duk masu karamin karfi ne da ke cikin halin naman taimako.