Shugaban hukumar hana yaduwar cututtuka na kasa (NCDC) Chikwe Ihekweazu ya bayyana cewa an sami raguwar yaduwar cutar kwalara a Najeriya.
Ya fadi haka ne ranar Asabar wa manema labarai a Abuja sannan ya kara da cewa banda jihohi takwas da suka yi fama da cutar babu inda cutar ta sake bullowa kuma.
Wadannan jihohi da suke fama da cutar sun hada da Adamawa, Bauchi, Kano, Katsina, Zamfara, Kogi, Plateau da Kaduna. Sannan har zuwa yanzu babu rahoton bullowar cutar a jihohin Anambra, Nasarawa da Yobe kuma.
” Mun sami rahotan cewa tun bulowar cutar a farkon shekarar nan mutane 16,008 ne suka kamu da cutar sannan 186 sun rasu.
” Bincike ya nuna cewa a Najeriya cutar kwalara kan bullo sau biyu a shekara wato lokacin damina da rani.”
Ihekweazu ya bayyana cewa hanyar kubuta daga kangi wannan cutar shine yin amfani da tsaftataccen ruwa da kuma tsaftace muhalli.
” Za kuma mu hada hannu da gwamnatin kasashen yankin tafkin Chadi don ganin mun dakile yaduwar wannan cuta’’.
A karshe Ihekweazu ya ce za su hada hannu da WHO,UNICEF,NPHCDA da sauran kungiyoyin bada tallafi don yi wa mutane allurar rigakafin wannan cutar a duk jihohin da cutar ta bullo a kasar nan.
Discussion about this post