Sanata Abu Ibrahim daga jiyar Katsina ya bayyana dalilan da yasa zai yi wuya kudirin kafa ‘yan sandan jihohi ya iya tsallake majalisar kasa.
Sanatan wanda kuma shi ne shugaban Kwamitin Harkokin ‘Yan sanda, ya ce akwai fargabar gwamnoni za su rika amfani da su suna musguna wa jama’a musamman masu adawa.
Ya ce zuwa yanzu an karanta kudirin a karo na farko ne kawai tukunna. Sai dai kuma tabbas akwai matsala gagaruma da ke gaban ‘yan majalisa domin kuwa zai yi wuya su amince da kudirin.
” A yanzu haka ina da tabbacin cewa mafi yawa daga cikin ‘yan majalisar kasar nan ba za su amince da wannan kudiri ba. Idan ka duba musamman yanki Arewa, nan ne kila akafi samun matsala, amma kudu suna da dan hadin kai da kila su iya amincewa da ita.
” Bayan haka kuma, maganar kudin rike su da kula da ayyukan su, wato albashi da alawus- alawus. Ana tare ma a dunkule abin yakan sami dan tangarda ballantana ace wai jihohi ne zasu rike su dundurungun.
” Albashi kawai ma ai kila sai anyi ta kai ruwa rana. Duk irin wadannan matsaloli ne zai iya dakile shirin samun amincewar majalisa wannan kudiri.
Abu Ibrahim ya kara da cewa duk da kyawawan manufofin wannan kudiri, babban abin da yake tada wa ‘yan majalisa hankali a kai shine rashin samun natsuwa da kafa ‘yan sandan jihohi.
” Wasu na ganin da zarar wani abu ya hada ka gwamna ko banbancin ra’ayi na siyasa zai iya wulakanta ka kai tsaye saboda karfin da yake dashi na gwamnan jihar.
” Idan aka ce za a bi yadda ake raba arzikin kasa ne, ina ganin jihohin Legas, Ribas, Kaduna, Kano, Akwa Ibom ne kawai za su iya biyan ‘yan sandan. Tsakani da Allah idan dai za a fadi gaskiya, kirkiro da ‘yansanda jihohi da irin wadannan kudaden da ake samu a kasa a raba wa jihohi, ba zai isa a iya rike su ba.
Discussion about this post