Ban dauki nauyin gangamin kamfen din Atiku a Adamawa ba – Gwamna Bindow

0

Gwamnan jihar Adamawa Jibirilla Bindow ya karyata rahoton wani Jarida dake yada labaran sa a yanar gizo cewa wai ya kashe wa gamgamin kamfen din Atiku naira miliyan 70.

Idan ba a manta ba a jiya Asabar ne a Yola Atiku Abubakar ya yi taron gangamin kaddamar da muradin sa na so ya zama shugaban kasa a Najeriya, a inuwar jam’iyyar PDP.

Daya daga cikin masu taimakawa gwamna Bindow a harkar yada labarai Martins Dickson ya bayyana cewa wannan zancen makiya ne da masu neman magana kawai.

” Wanda ya rubuta wannan labari ba shi da abin yi ne shine ya sa ya kirkiro karya ya ke ta yadawa domin ya shafa wa gwamna Bindow bakar tawada, amma ba ayi haka ba.

” Irin wadannan labarai ba zai karkatar da mu daga ci gaba da yi wa mutane aiki kamar yadda gwamna yayi musu alkawari kuma ya dukufa yana yi.

” Kowa dan jihar Adamawa zai shaida irin ayyukan da gwamna Bindow yake yi a jihar kuma masu irin wadannan rubuce-rubuce na yi ne don su kawo wani abin da ba haka a siyasar jihar.” Inji Dickson.

Share.

game da Author