Gobara ya cinye shaguna 217 a kasuwar Taminus da ke Jos

0

Gobara da ya fara ci tun da karfe 1:30 na dare ya babbake shaguna sama da 200 a babbar kasuwar Taminus dake garin Jos Jihar Filato.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Filato Undie Andie ya tabbatar wa manema labarai aukuwar gobarar.

Ya ce ‘yan sanda sun iya kubutar da wasu kaya daga kasuwar kuma duk suna ofishin su. Da zaran an kammala tantance masu shi za amika musu.

Shugaban ‘yan kasuwan Taminus Jimoh Yusuf ya ce akalla shaguna 217 ne suka kone sannan akwai wani da ya rasa kayan kusan naira miliyan 28.

” Akwaine 166 da ya basu jarin naira 180,000 da dukkan su suna dan yin kananan sana’oi kuma duk ya shafe su wannan gobarar.

Shugaban masu kananan sana’oi a kasuwar Mustapha Ibrahim ya ce ‘yan kasuwa sun rasa kayan sama da miliyan 70.

Share.

game da Author