Wasu masu bincike daga kasashen Najeriya da Britaniya sun gano cewa mutane a duniya na yin amfani da magunguna ‘Antibiotics’ ba tare da samun izini daga likita ba.
Sukan garzaya shagunan magani dake kusa da su kawai su siya magani ba tare sun ga likita ba saboda babu doka da zai hana hakan a kasashen duniya da dama.
Daya daga cikin wadanda suka gudanar da wannan bincike Emmanuel Adewuyi ya bayyana cewa sun sami wannan sakamako ne daga binciken da suka gudanar a kasashe 24 a duniya.
Adewuyi ya bayyana cewa illar amfani da magani ba tare da izinin likita ba na hana maganin warkar da cutar da ya kamata sannan yakan sa a iya samun wata cutar.
” Bincike ya nuna cewa a kasar Amurka duk shekara mutane sama da miliyan biyu na kamuwa da cututtuka da ya shafi shan magani ba bisa ka’ida ba sannan kuma mutane da dama na rasuwa a dalilin haka.
” Mun kuma gamo cewa a mafi yawan lokuta samun yawa-yawan shagunan siyar da magani a ko ina ne ke haddasa irin wannan matsala inda mutum da zarar ya bushi iska zai garzaya ya siya magani kuma a bashi ba tare da umarnin likita ba.”