Babban Mai binciken Kudi na Najeriya, Anthony Ayine, ya shawarci Gwmantin Najeriya da ta yi amfani da doka ta halasta Asusun Rarar Ribar Danyen Man Fetur, da ake kira Excess Crude Account.
Wannan bayani ya na kunshe ne a cikin wani rahoto da Ayine ya fitar bayan karkare bin diddigin kudaden da gwamnatin tarayya ta kashe a cikin 2016.
An fitar da wannan rahoto a cikin watan Yuni, kuma shi ne rahoton baya-bayan nan da aka fitar dangane da kudaden da tarayya ke kashewa a kowace shekara.
Cikakkun bayanan da suka fado a hannun PREMIUM TIMES a ranar Litinin da ta wuce, sun tabbatar da cewa an zaftare har sama da naira bilyan 361 daga cikin kudin shigar ko ribar man fetur da kuma gas a shekarar 2016.
Rahoton ya tabbatar da cewa an cire su ne tun kafin a biya Gwamnatin Tarayya balas din ta da sunan an ciri kudin Rarar Ribar Danyen Mai.
“Wadannan kudade da aka cire kuma an karya dokar kasa sashe na 162 (1) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999. Domin wannan sashe cewa ya yi gwamnatin tarayya ta bude Asusun Tarayya kawai, wato Federation Account, wanda a cikin sa ne kawai za a rika zuba dukkan wasu kudin shiga na Gwmnatin Tarayya, bai ce a rika zubawa cikin wani asusu wai shi Asusun Rarar Ribar Danyen Mai ba.”
Ayine ya ce an dade ana tafka wannan kuskure, tun daga 2007 har yau kuma ba a samu wata gwamnati ta warware wannan sarkakiya ba.
Gwamnonin Kasar nan na amfana daga wannan asusu, inda ake kasafta musu ribar a kowane wata.
Dama kuma cikin watan Nuwambar da ya gabata, Majalisar Dattawa ta ce wannan asusu haramtacce ne, domin babu abin da ake tafkawa ciki sai samar wa gwamnoni kudaden da suke barje gumen su son ran su.