Abin da muka tattauna da Shugaba Buhari -‘Yan Majalisa

0

Mambobin Majalisar Tarayya masu goyon bayan Shugaba Muhammadu Buhari 100 bisa 100, sun bayar da karin haske dangane da ganawar da suka yi da shugaban a cikin sirri, a jiya da yamma.

Hon. Sarkin Adar da Abdulmumin Jibrin ne suka yi musu jagora wurin ganawa da Buhari.

Da ya ke ganawa da manema labarai bayan kammala ganawar, Sarkin Adar ya ce sun kalli damuwar da ke cikin zukayan ‘yan Najeriya, da kuma halin da sauran jam’iyyu ke ciki, ganin cewa zabe ya gabato.

Adar ya kara da cewa a matsayin sa na jigon ‘yan APC a Majalisar Tarayya, ya ga cewa akwai matukar bukatar ganawa da shugaba Buhari da kuma shugaban jam’iyyar APC domin a shawo kan damuwar da ke zukatan mambobin fadin tarayyar kasar nan.

Ya ci gaba da cewa maganar gaskiya su na da damuwa sosai musamman a kan yadda aka gudanar da zabukan shugabannin jam’iyya, tun daga mazabu, har zuwa shugabannin kananan hukumomi da shugabannin jam’iyyu na jihohi.

“Akwai koke-koke da korafe korafe daga wadanda ke ganin cewa an zalunce su, ko kuma ba a yi musu adalci ba. To ganin cewa ba a saurare suba, shi ya sa su ke ta kokarin ganin sun fice daga jam’iyyar APC.

“Duk da wannan, mu dai muka ga cewa za mu ci gaba da zama cikin APC, amma akwai bukatar mu samu shugaba Buhari mu sanar da shi cewa a gaggauta magance wadancan matsalolin, domin su kuma su je su yi ta gaganiyar shawo kan wadanda ke niyyar ficewa din, su hakura su zauna a cikin jam’iyyar.

Sarkin Adar wanda ke wakiltar Kananan Hukumomin Goronyo da Gada daga jihar Sokoto, ya ce sun san masu haddasa wannan rarrabuwar kawuna a cikin APC, don haka su yi kokarin ganin hakan ba ta sake faruwa ba.

Da aka tambaye shi irin amsar da Buhari ya ba su, Adar ya ce shugaba Buhari ya karbe su hannu bibbiyu, kuma ya yi jawadan da suka kamata ya yi sosai.

Daga nan kuma sai ya ce sun dauki tsawon lokaci wajen bayayyana wa Buhari muhimmanci da ma’anar ayyukan raya mazabu da ake bai wa ‘yan majalisa a cikin kasafin kudi, wanda a koda yaushe ake samun rashin fahimta a kan sa.

Ya ce sun shaida wa Buhari cewa ba fa zunzurutun ruwan kudi ne ake bai wa ‘yan majalisa su je su yi aiki ba, a’a. Su dai ne ke fadin irin ayyukan da za a yi da kuma wuraren da za a yi su kawai.

Daga nan ya ce da irin wadandan ayyukan ne kawai jama’a musamman na cikin karkara za su sani kuma za su ga cewa gwamnatin tarayya ta matso kusa da su.

Shi ma Hon. Abdulmumin Jibrin ya ce ganawar da suka yi da Buhari ta yi matukar muhimmanci sosai.

Ya ce Buhari ya dauki lokaci shi ma ya na yi musu bayanin kokarin da ya ke yi wajen ganin ya kara inganta Najeriya fiye da yadda ta ke a yanzu.

Share.

game da Author