DASUKI: Dalilin da ya sa gwamnati ba ta bi umarnin kotu ba – Malami

0

Ministan Shari’a Abubakar Malami ya bayyana cewa babban dalilin da ya sa gwamnati ta ke sabawa umarnin kotu game da Sambo Dasuki shine don cin amanar kasa da yayi.

A hira da yayi da VOA Hausa, Malami ya ce abin dubawa a cikin wannan cece kuce da ake tayi shine a gane fa shi Sambo Dasuki mutum daya ne tal, sannan laifi ne yayi wa ‘yan Najeriya kuma ya shafi mutanen kasar ne gaba daya.

Ya ce a duk kasashen duniya anyi ittifaki cewa laifin da ya shafi mutanen kasa wato masu yawa ya fi tasiri kan na mutum daya domin kuwa gwamnati na jama’a ne.

Idan ba a manta ba sau biyu kenan kotu na yi wa gwamnatin Najeriya umarnin a saki Sambo Dasuki ta hanyar bada belin sa amma gwamnati tayi burus da wannan umarni.

A bisa wadannan dalilai ne ya sa ake ta korafi, cece-kuce, kan kin bin doka da wannan gwamnati tayi duk da irin ikirari da yekuwa da take yi cewa ita gwamnati ce mai bin doka da Oda.

Malami ya yi karin bayani cewa a sanadiyyar rashin kishin kasa da nuna halin ko-in-kula ya sa aka sami baraka a harkar tsaro a kasar nan.

” A dalilin haka yasa an rasa mutane sama da 100,000 a kasar nan, sannan kudaden da ya kamata a siya makamai da su wa sojojin Najeriya ba ayi haka ba.”

Wanda sune sanadiyyar matsalolin da aka samu a kasa Najeriya duk a karkashin shugaban cin sa shi Dasuki, kamar yadda ya ambato.

Malami ya ce gwamnatin Buhari gwamnati ce mai bin doka ce sannan kuma idan har ya kai ga ana ta ja a kotu da har ya kai ga gwamnati ta daukaka kara, zata bi doka domin ita mai bin doka ce.

Share.

game da Author