A yammacin Alhamis ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi ganawar sirri da shugaban majalisar Dattawa, Bukola Saraki da wasu gwamnoni hudu.
Gwamnonin sun hada da gwamnan Kebbi, Abubakar Bagudu, Ogun, Ibikunle Amosun, gwamnan Katsina, Aminu Masari da gwamnan jihar Zamfara, Abdul-Aziz Yari.
Bayan wadannan gwamnoni, zababben gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi ya halarci ganawan.
Ganawar da ta dauki tsawon mintuna 45, babu wani da ga cikin wadanda suka halarce ta da ya tsokata wa manema labaran fadar shugaban kasa abin da aka tattauna a ganawar.