‘Yan fashi sun kashe wani dan sanda a Nasarawa

0

A jiya Laraba ne jami’in harka da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa Samaila Usman ya bayyana cewa wasu ‘yan fashi sun harbe daya daga cikin ma’aikatan su.

Usman ya sanar da haka ne a garin Lafia.

Ya ce wannan abu dai ya faru ne ranar 15 ga wannan watan bayan ‘yan sandan sun yi arangama da wadannan nan ‘yan fashi a hanyar Akwanga-Wamba.

” Ma’aikatan mu sun yi arangama da ‘yan fashi a lokacin da suka yi kicibis da shingen da barayin suka kafa sannan su barayin suka harbe dan sanda daya.

” Mun harbe dan fashi daya kuma sauran sun gudu da raunin harsashi a jikkunan su sannan mu kuma muna iya kokarin mu don ganin mun kamo sauran.”

A karshe Usman ya yi kira ga mutanen Akwanga-Wamba da su gaggauta kai karar duk wanda suka ganshi da rauni harsashin bindiga ofishin ‘yan sanda mafi kusa.

Share.

game da Author