Sanata Dino Melaye yayi Allah wadaran wadanda suka kona ajujuwan da ya gina wa dalibai a makarantar Sakandare dake sarkin Noma, Lokoja.
An dai wayi gari ranar Laraba ne aka ga wasu sabbin ajujuwa da sanata mai wakiltan Kogi ta Yamma Dino Melaye ya gina da zai kaddamar ranar Alhamis a kone kurumus.
Bayanai da suka iske mu, har yau ba a san ko su wane suka banka musu wuta suka kone kurmus ba.
Melaye ya gina ajujuwan guda biyu ne a Makarantar Sakandare ta Sarkin Noma, da ke Lokoja.
Melaye ya ce bai ga dalilin da zai sa a dauki wasu abubuwan a maida su siyasa ba domin kuwa wannan bai kamata ba ko kadan.

” Don wai wasu ‘yan ta’adda sun kona makarantar da na gina bazai hanani ci gaba da yi wa mutanen jihar Kogi aiki ba kamar yadda na yi alkawari. Sannan ina so su sani cewa tabbas zan sake gina wadannan ajujuwa da aka kona sannan zan ci gaba da rangadin kaddamar da ayyuka sama da 100 da nayi wa mutane.”
Dino ya ce babu abin da zai hana shi ci gaban da rangadin mazabar sa da kaddamar da ayyuka sama da 100 da yayi musu cikin shekara uku da suka tura shi majalisa.

Discussion about this post