An tsinci gawar amarya Hindatu Yahaya da ruwa ya ci a ambaliyar Jibiya. An tsinci gawar ta ne a cikin Jamhuriyar Nijar.
An daura mata aure ne tare da angon ta Sani Yahaya, kwana uku kacal kafin afkuwar ambaliyar da ta yi gaba da ita.
“An tsinci gawar amarya ta a kauyen Girka da ke yankin Mada Rumfa cikin Jamhuriyar Nijar.” Inji shi.
Ya Yahaya ya ce ambaliyar da ta faru ranar Litinin da misalin karfe 2 na dare ne ta tafi da amaryar tasa, tare da shafe gidan sa.
“Mun yi ta faman neman gawar ta a cikin kogi da kuma cikin burbushin rugurguzajjen ginin bangon gida na, amma ba mu same ta ba.
“To mu na cikin nema ne sai muka ji karan waya daga wasu da ke taya mu nema a Mada Rumfa, cikin Jamhuriyar Nijar, cewa sun ceto wata gawa ta wata matashiyar mata da ruwa ya bi da ita ta garin su.
“Da muka garzaya garin, sai muka ga lallai gawar amarya ta ce da ruwa ya tafi da ita.
“Mun karbo gawar ta, kuma muka zo da ita nan Jibiya, muka yi mata Sallah aka bizne ta.” Inji Yahaya.
“Yahaya ya ce kwanaki uku ya kasa cin abinci, saboda jimami da damuwar bacewa matar ta sa.
Idan za a iya tunawa, Gwamnan Katsina Aminu Masari, ya bayyana cewa a lokacin da ya je jaje a Jibiya, ya tausaya wa wani ango da ya ga ya na ta neman amaryar sa wadda duka-duka kwana uku da tarewar ta a gidan sa.