Shugaban hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko na babban birnin tarayya Abuja Rilwanu Mohammed ya bayyana cewa hukumar ta zabi wasu asibitoci 50 da za su yi aiki na tsawon awowi 24 a Abuja.
Ya fadi haka ne ranar Talata da ya ke hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Abuja.
” A mafi yawan lokutta mutane musamman mazauna karkara kan tafi asibiti cikin dare. Sau da yawa ko da sun tafi basu samun likitoci ko ma’aikatan asibitin. Saboda haka ne ya sa mu ka zabi wadannan asibitoci 50 domin su rika aiki har safe.
Sannan kuma gwamnati na kokarin kara gina cibiyoyin kiwon lafiya 12 a yankuna shida dake a Abuja.