Tsohon babban jojin Najeriya Aloysious Katsina-Alu ya rasu bayan fama da ‘yar gajeruwar rashin lafiya da yayi a asibiti a Abuja.
Maitaimakawa babban Jojin Najeriya Walter Onnoghen, Awassam Bassey, ya tabbatar da rasuwar marigayi Katsina-Alu inda ya bayyana cewa rijistarar Kotun kolin Najeriya Hadizat Mustapha ne ta sanar da shi haka.
Marigayi Katsina-Alu haifaffen garin Ushongo, jihar Benuwai. Ya zama alkali a Kotun Koli a 1998 sannan ya zama babban Jojin Najeriya a 2009.
Discussion about this post