Babban sakataren ma’aikatar ruwa na jihar Sokoto Hussaini Umar ya bayyana cewa asusun kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya (UNICEF) ta gina bandakuna 222 da haka rijiyoyin burtsatse 201 a wasu zababbun kananan hukumomi a jihar.
Umar ya sanar da haka ne ranar Talata a garin Sokoto a wani zama da gwamnati ta yi da UNICEF.
Umar ya ce UNICEF ta gina bandakunan ne domin samar wa mutane da wuraren zagawa da sukan yi a waje sannan ta haka rijiyoyin burtsatsen ne domin samar da tsaftataccen ruwa wa mutanen jihar musamman mazauna kananan hukumomi.
Ya ce rijiyoyin butsatsen da UNICEF ta gina sun hada da na tuka-tuka da wanda ke amfani da hasken rana sannan asusun na kokarin gyara wasu rijiyoyin burtsatsen da suka lalace a wasu zabbabun kananan hukumomin jihar.
” Mun kuma hada guiwa da UNICEF don horar da matasa sana’o’in hannu da inganta aiyukkan ma’aikatan gwamnati a jihar sannan gwamnati ta samar da Naira miliyan 400 domin ganin an sami nasara kan haka.
Bayan haka babban sakataren ma’aikatar kiwon lafiya na jihar Mustapha Ali ya ce gwamnati ta ware Naira miliyan 150 domin samar da magungunan inganta kiwon lafiyar mutanen dake fama da yunwa a jihar.
” Sannan mun yi wa kashi 40 bisa 100 na yara kananan allurar rigakafi a jihar kuma mun dauki matakan da za su taimaka wurin wayar da kan mutane sanin mahimmancin yi wa ‘ya’yan su rigakafi.”
A karshe babban sakataren ma’aikatar kasafin kudi na jihar Aminu Dikko da jami’in UNICEF Muhammadin Pall sun bayyana cewa sun shirya wannan zama ne domin gano da warware kalubalan da akan yi fama da su a fannonin kiwon lafiya, Ilimi, ruwa, tsaftace muhalli da sauran su a jihar.