Buhari ya gabatar wa Majalisa kasafin kudin zaben 2019

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana wa Majalisar Tarayya cewa Najeriya na bukatar akalla naira biliyan 254, 445, 322, 600.00 domin gudanar da zaben 2019.

Wannan bayani na kunshe ne a cikin wasikar da Buhari ya aika wa Majalisar Dattawa.

Wasikar dai na kunshe da kasafi da kuma jadawalin kudaden da za a kashe, inda za a kashe su da kuma yadda za a kashe su a kowane bangare da ke da hannu wajen tabbatar da an gudanar da zaben 2019 cikin kwanciyar hankali.

Wasikar dai kamar yadda shugaban kasa ya rattaba, ta kara da cewa za a fitar da wadannan kudade ne daga cikin kasafin 2018 da kuma na 2019 da za a yi nan gaba.

Wannan kasafin kudin zaben na 2019 dai za a karkasa su ne ga hukumomin gwamnatin tarayya har guda shida, inda Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ce ke da kaso mafi tsoka da ya kai har naira biliyan N189, 207, 544, 893.00

Ga jadawalin inda za a kashe kudaden yayin zaben na 2019, kamar yadda Buhari ya rattawa wa Majalisar Dattawa, kuma ya nemi amincewar ta.

1 – HUKUMAR ZABE MAI ZAMAN KANTA TA KASA (INEC)

Naira Biliyan 143, 512, 529, 445: Daga Kasafin 2018.

Naira Biliyan 45, 695, 015,438: Daga Kasafin 2019.

JIMLA: N189, 207, 544, 893.

2 – OFISHIN MAI BA SHUGABAN KASA SHAWARA A KAN TSARO

Naira Biliya 3, 855, 500, 000: Daga Kasafin 2018.

Naira Biliyan 426, 000, 000: Daga Kasafin 2019.

JIMLA: Naira Biliyan 4, 281, 500,000

3 – JAMI’AN TSARO NA DSS

Naira Biliyan 2, 903, 638, 000: Daga Kasafin 2018

Naira Biliyan 9,309,644,455: Daga Kasafin 2019

JIMLA: Naira Biliyan 12, 213, 282, 455

4 – JAMI’AN NSCDC

Naira Biliyan 1, 845, 597, 000: Daga Kasafin 2018

Naira Biliyan 1, 727, 997, 500: Daga Kasafin 2019.

JIMLA: Naira Biliyan 3, 573, 534, 500

5 – ‘YAN SANDAN NAJERIYA

Naira Biliyan 11, 457, 417, 432: Daga Kasafin 2018

Naira Biliyan 19, 083, 900, 000: Daga Kasafin 2019

JIMLA: Naira Biliyan 30, 541, 317, 432

6 – HUKUMAR LEKEN ASIRI

Naira Miliyan 530, 110, 078: Daga Kasafin 2018

Naira Biliyan 2, 098,033, 142: Daga Kasafin 2019

JIMLA: Naira Biliyan 2, 628, 143, 320

JIMILLA DAGA KASAFIN 2018: Naira Biliyan 164, 104, 792, 065

JIMILLA DAGA KASAFIN 2019: Naira Biliyan 78, 314, 530, 535

JIMILLA GABA DAYA: Naira Biliyan 242, 445, 322, 600

Share.

game da Author