Cincirindon matasan Jalingo sun yi wa Kwamishinan ‘Yan sandan Jihar, David Akinremi ruwan duwatsu a Jalingo.
Kakakin Rundunar ‘yan sandan jihar, David Misal, ya bayyana wa manema labarai a Jalingo cewa kwamishinan ya je unguwar Tudun Wada ne da kan sa domin ya kwantar da tarzomar da aka ce matasan unguwar su na yi.
“An jefe shi da dutse, kuma rotsen da aka yi masa ya zubar da jini mai yawa, har sai da aka garzaya da shi asibiti, amma an sallame shi.
“Tun jiya ne matasan unguwar suka fara tada hankulan mutenen yankin tare da amfani da makamai irin su adda, takobi, da gatura. An yi Tudun Wada da Gadan Boboji.
“Jami’an mu sun je sun kwantar da rikicin. Amma yau kuma sai matasan suka sake fitowa dandazo mai yawa fiye ma da jiya. Suka rika kai wa jama’a farmaki.
“Abin ya yi munin da sai da Kwamishinan ‘Yan san da da kan sa ya je.
Ya ce ya na cikin yi wa yaran jawabi ne, sai kawai ya ji wani ya kwamtsa jifa a goshin sa, ‘kau’. Jinin da ya rika kwarara ne ya sa tilas sai da aka garzaya da shi asibiti.”
Rundunar ‘yan sandan ta ce ba za su taba bari wasu batagari su hana jama’a zaman lafiya a jihar ba.