Gamayyar kungiyoyin goyon bayan Buhari sun nada Sheriff babban daraktan su

0

Gamayyar Kungiyoyin Goyon Bayan Buhari a yakin neman zaben 2019, sun bayyana cewa sun yanke shawarar nada tsohon gamnan Jihar Barno, Sanata Ali Modu Sheriff a matsayin babban darakatan kamfen din su.

Gamayyar Kungiyoyin da ake kira ‘Presidential Support Committee of Buhari 2019, kungiyoyi ne da suka haura 300 da ke da rajista a karkashin Mai Taimaka Wa Shaugaban Kasa a Kan Harkokin Siyasa.

Sakataren ta na Kasa, Kassim Kassim, ya ce sun zabi Sheriff domin alheri ne ga kungiyar, kuma hakan shi ne mafi dacewa a gare su.

Da ya ke magana a Abuja, Kasim ya ce ba rundunar kamfen din shugaba Muhammadu Buhari dungurugum ce Sheriff zai jagoranta, kamar yadda aka bayyana a baya ba.

Ya ce kungiyar na ta kokarin ganin ta gudanar da gagarimin tasiri a tafiyar Buhari ta zaben 2019, musammamn ganin yadda matsaloli suka dabaibaye jam’iyyar APC kwanan nan.

Daga nan sai ya kara cewa ba gaskiya ba ne da ake yi musu mummunar fahimta cewa kunguyar su za ta zama kishiya ga kwamitin yakin neman zaben da Ministan Harkokin Sufuri, Rotimi Ameachi zai jagoranta.

Idan ba a manta ba Sakataren gwamnatin tarayya ya fito ya karyata nada Ali Modu Sheriff shugaban kungiyar Kamfen din Buhari, da wani hadimin Buhari ya sanar.

Hadimin Buhari dake shine mataimakin mai ba shugaba Buhari shawara kan harkar siyasa Gideon Sammani ya sanar cewa an kafa wata sabuwar kwamiti da Ali Modu Sheriff zai shugabanta.

Cikin kwamaitin har da su Mamman Daura, Mawaki Rarara, Ireti Kingibe da wasu jiga-jigan APC da makusantan shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ko da yake ko a wancan sanarwar an bayyana cewa kwamitin ba irin wacce ministan Sufuri Rotimi Amaechi yake jagoranta bane, amma dai kusan duk wani mai iko a Jam’iyyar APC yana cikin wannan sabuwar kwamiti.

Kakakin ofishin sakataren gwamnatin tarayya da ya sa hannu a takardar karyata kafa wannan kwamiti na Ali Sheriff, Lawrence Ojabo, ya kara da yin kira ga jama’ a su yi watsi da wannan sanarwa don ko ba a kafa wata kwamiti mai kama da haka ba, shirga wa ‘yan Najeriya ne kawai hadimin Buhari yayi.

Share.

game da Author