Hukumar Tsaro ta Sojojin Najeriya ta karyata labarin cewa sojoji 23 sun salwanta tare da motoci takwas a harin da Boko Haram suka kai musu a cikin Karamar Hukumar Bama ta jihar Barno.
An dai kai harin ne a ranar Juma’a, sai dai kuma sojoji ba su bayyana kai musu harin da aka yi ba, har sai da kafafen yada labarai suka buga tukunna a ranar Lahadi.
Sai dai kuma kakakin sojojin, Texas Chukwu, ya tabbatar da kai harin, amma ya ce an yi karin gishiri sosai a cikin labarin da aka watsa.
Birgadiya Chukwu ya ce tabbar an kai wa sojoji hari a ranar Juma’ar da ta gabata, amma fa ba a kashe sojoji ko daya ba. Kuma babu wadanda suka bata.
Ya ce sojojin ne ma suka kashe mahara har 22. Haka ya shaida wa manema labarai a dakin taron sojoji.