Za a kwace mana gidajen mu a Kaduna, Inji masu zanga-zanga

0

A Safiyar yau Litini ne wasu mazauna kauyukan da ke zagaye da garin Rigachikum, karamar hukumar Igabi, jihar Kaduna suka fito zanga-zanga, inda suka tare babbar titin Kaduna zuwa Zaria, suna neman gwamnati ta kawo musu dauki.

Motocin haya musamman wadanda suka nufi Abuja sun yi cincirundo a wannan gari inda masu zanga-zangar suka ki bari kowa ya wuce.

Sun koka cewa rundunar Sojin Najeriya ce ke kokarin kwace musu gidajen su da karfin tsiya.

Wata mata da ta zo wannan wurin tare da ‘ya’yan ta hudu ta bayyana mana cewa ba daidai bane yadda sojojin ke kokarin kwace musu inda suke zaune tun fil azal.

” Mijina ya mutu ya barni da wadannan ya’ya yanzu idan sojojinan suka kwace mini wurin zama ina zani da su.”

Masu zanga-zangar sun shaida wa wakiliyar PREMIUM TIMES HAUSA da ke wannan wuri a lokacin cewa sun hada wannan zanga-zanga ne domin jawo hankalin gwamnati ta dube su da idon rahama.

Ana haka ne dai Sojoji suka fito suka fatattaki wadannan masu zanga-zanga, daga nan motoci wasu da suka shafe kusan awowi a wannan wuri suka fara wucewa.

Har yanzu dai babu wani jami’in gwamnati ko na sojan Najeriya da ya ce komai a kai.

Share.

game da Author