RASHA 2018: Za a fafata da Ahmed Musa a cin kyautar kwallon da ta fi kowace birgewa

0

FIFA ta zabi dan wasan Super Eagles, Ahmed Musa, cikin wadanda za su fafata cikin kwallon da aka fi nuna bajinta, kwarewa da kuma bugrgewa wajen jefa ta raga a gasar cin Kofin Duniya na 2018, da aka kammala jiya Lahadi a Rasha.

A gasar ta bana dai an jefa kwallaye 167, amma 18 daga cikin su kadai FIFA ta tsame domin a fitar da mafi birgewa da nuna kwayewa a wajen jefa ta raga.

Kwallon da Musa ya ci ta biyu, a wasan Najeriya da Iceland ce aka dauka. Dama kwallaye biyu ya ci a wasan na Najeriya da Iceland din.

Cikin wadanda aka zaba har da kwallo ta uku da Cristiano Ronaldo ya ci Spain da kuma kwallon da Messi ya ci Najeriya.

Akwai kwallon da dan wasan Rasha. Denis Cheryshev ya ci, haka ta wani dan wasan Rasha din mai suna Artem Dzyuba.

Sauran kuma sun hada da:

Cristiano Ronaldo, Portugal ( v Spain);

Nacho, Spain (v Portugal);

Philippe Coutinho, Brazil (v Switzerland);

Dries Mertens, Belgium (v Panama);

Juan Quintero, Colombia (v Japan);

Luka Modric, Croatia (v Argentina);

Ahmed Musa, Nigeria ( v Iceland);

Lionel Messi, Argentina (v Nigeria);

Toni Kroos, Germany (v Sweden);

Jesse Lingard, England (v Panama);

Ricardo Quaresma, Portugal (v Iran);

Adnan Januzaj, Belgium (v England);

Angel Di Maria, Argentina (v France);

Benjamin Pavard, France (v Argentina);

Nacer Chadli, Belgium (v Japan).

Share.

game da Author