PDP ta ki amincewa da sakamakon zaben gwamnan Ekiti

0

Jam’iyyar PDP ta kasa, ta tabbatar da kin amincewa da sakamakon zaben da INEC ta bayyana cewa dan takarar jam’iyyar APC ne, Kayode Fayemi ya lashe zaben.

A cikin wata takardar da taraba wa manema labarai a jiya Lahadi da yammaci, PDP ta yi zargin cewa an tafka magudi wajen dumbuza wa APC kuri’u masu tarin yawa, ta yadda aka bada sanarwa cewa APC din ce ta yi nasara.

“Daga sahihan sakamakon da suka rika fitowa daga rumfunan zabe a fadin kasar, a fili ya ke cewa dan takarar PDP, Farfesa Kolapo Olusola-Eleka ne yayi nasarar lashe zaben da rata mai yawa.

“Daga cibiyar tattara sakamakon zabe a ofishin INEC aka yi aringizo ga APC”. Inji kakakin yada labaran PDP na kasa.

Cikin takardar da PDP ta fito mai taken “ba a isa a murtsike mu ba”, ta ce sakamakon zaben kirkirarre ne kuma jabu ne, ba na gaskiya ba ne.

“Sakamakon da aka ce dan takarar APC Kayode Fayemi ya yi nasara a kan PDP, fashi da makami ne, yi wa al’umma fizge ne, kuma karya fukafikin dimokradiyya ne da tsana kuru-kuru.”

“Duniya ta shaida yadda gwamnati ta yi amfani da jami’an tsaro da na INEC aka yi sumogal din kuri’un bogi ga APC ta hanyar baddala sakamakon zabe na halas. An kuma yi amfani da jami’an tsaro an kori ejan-ejan na PDP inda daga nan aka fara baddala sakamakon zaben.

Daga nan sai PDP ta yi tuni da abin da ta kira mummunan kalamin da Shugaban Jam’iyyar APC, Adams Oshimhole ya fukta cewa za su ‘kulle PDP a cikin keji a Ekiti.”

A karshe PDP ta ce za ta dauki mataki na gaba domin kwato hakkin ta daga ‘yan fashin sakamakon zaben Ekiti da rana tsaka.

Bayan haka kuma shi kansa dan takarar gwamnan jihar na PDP Eleka ya bayyana cewa zai garzaya kotu domin abi masa hakkin sa.

Share.

game da Author