“Ina taya ka murna Fayemi, Jama’ar ka sun yi maka halacci” – Inji Obasanjo

0

Tsohon shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya aika da sakon taya murnar ga sabon gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi.

A sakon sa Obasanjo ya bayyana cewa tabbas mutanen jihar Ekiti sun nuna wa Fayemi na jam’iyyar APC halacci saboda haka yayi kira gare shi da ya yi musu shima.

” Na yi matukar farinciki game wannan nasara da kasamu. Mutanen jihar Ekiti sun nuna maka suna tare da kai kuma suna kaunar ka. Shawara ta gareka shine ka tabbata ka yi musu halacci kamar yadda suka yi maka.

” Ka yi aiki tukuru domin inganta rayukan mutanen jihar ka sannan ka jawo abokan hamayyar ka kusa da kai ku hada kai domin ci gabar jihar.

Duk da dai Obasanjo baya tare da Jam’iyyar APC, a wannan zabe dai yayi APC ne.

Dama can ba a shiri tsakanin Obasanjo da tsohon gwamna Fayose, domin a lokacin sa ne aka taba tsige shi daga gwamnan jihar. Sannan kuma shima Fayose din baya raga wa Obasanjo wajen ci masa mutunci karara.

Share.

game da Author