AN YANKA TA TASHI: Boss Mustapha ya karyata kafa kwamitin Ali Modu Sheriff

0

Kwasam kuma bayan sanar da kafa sabuwar kwamiti na kamfen din Buhari da har aka ce an nada tsohon gwamnan jihar Barno Ali Modu Sheriff shugaba sai gashi kuma sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya karyata kafa wannan kwamiti da nade-naden da aka ce an yi.

A jiya ne hadimin Buhari dake shine mataimakin mai ba shugaba Buhari shawara kan harkar siyasa Gideon Sammani ya sanar cewa an kafa wata sabuwar kwamiti da Ali Modu Sheriff zai shugabanta.

Cikin kwamaitin har da su Mamman Daura, Mawaki Rarara, Ireti Kingibe da wasu jiga-jigan APC da makusantan shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ko da yake ko a wancan sanarwar an bayyana cewa kwamitin ba irin wacce ministan Sufuri Rotimi Amaechi yake jagoranta bane, amma dai kusan duk wani mai iko a Jam’iyyar APC yana cikin wannan sabuwar kwamiti.

Kakakin ofishin sakataren gwamnatin tarayya da ya sa hannu a takardar karyata kafa wannan kwamiti na Ali Sheriff, Lawrence Ojabo, ya kara da yin kira ga jama’ a su yi watsi da wannan sanarwa don ko ba a kafa wata kwamiti mai kama da haka ba, shirga wa ‘yan Najeriya ne kawai hadimin Buhari yayi.

Share.

game da Author