Tsohon gwamnan jigar Barno sanata Ali Modu Sheriff ya zama Darektan kwamiti na musamman na kamfen din shugaba Muhammadu Buhari domin tunkarar zaben 2019.
Kamar yadda PR Nigeria ta ruwaito wannan kwamiti da bam yake da kwamitin da ministan Sufuri Rotimi Amaechi ya ke jagoranta.
A kwamitin akwai, Mamman Daura, Boss Mustapha, Bola Tinubu, Matthew Mbu, Ahmed Sani, George Akume, Abdullahi Adamu, da sanata Ita Giwa.
Sauran sun hada da Honarabul Gudaji Kazaure, Ireti Kingibe, Ismaila Funtua and Abu Ibrahim.
Shi kansa shugaba Buhari na cikin wannan sabuwar kwamiti.
Mawaki Dauda Kahutu Rarara an nada shi darektan waka a tafiyar.
Discussion about this post