Bangarorin jam’iyyar APC biyu a Jihar Kaduna da aka fi sani da APC Akida da kuma APC Restoration Group, sun bayar da sanarwar ficewa daga jam’iyyar APC.
Sun bayar da sanarwar a yau Alhamis a Kaduna bayan jam’iyyar APC, kamar yadda suka furta, ta kasa cika alkawurran da ta daukar wa ‘yan Najeriya.
Har ya zuwa yanzu dai ba su bayyana jam’iyyar da za su shiga su narke a ciki ba, amma sun bayyana cewa ana ci gaba da taron tuntubar juna tsakanin su da wasu jam’iyyun da akidar su ta zo daya.
Mista Tom Maiyashi ya ce hankalin su a kwance ya ke a halin yanzu, ganin yadda suka jefar da kwallon mangwaron APC, suka huta da kuda.
Shehu Sani na daya daga cikin mambobin wannan bangare na APC da suka fice daga jam’iyyar, amma dai bai halarci taron manema labaran ba.
Dama kuma daya daga cikin mambobin, Hakeem Baba-Ahmed ya fice daga jam’iyyar kwanan baya.
Wasu daga cikin yan kungiyoyin biyu sun hada da Hon Isah Ashiru, Tijjani Ramalan, Suleiman Hunkuyi da wasu jiga-jigan hasalallun ‘yan APC.