Kwastam ta kama bidigogi a tashar jiragen ruwa a jihar Legas

0

Shugaban hukumar kwastam dake kula da tasahr Tin-Can Island Command a jihar Legas, Musa Abdullahi ya bayyana cewa a ranar Litini da Talata hukumar ta kama makamai da dama a tashar jiragen ruwa dake TinCan.

Ya fadi haka ne wa manema labarai ranar Laraba a jihar Legas.

” A ranar Litini ne hukumar mu ta kama wata kwantena da aka loda ta da bindigogi da wukake. Sannan a ranar Talata yayin da muke duba wasu motocin da aka shigo da su a tashar muka tsinci wata bakar leda dake dauke da harsasai.

Abdullahi ya ce sun danka wa fannin zantaswa na hukumar domin ci gaba da bincike a kan su.

Share.

game da Author