Za a raba gidajen sauro wa mutane kyauta a jihar Jigawa

0

Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Jigawa Abba Zakari ya bayyana cewa gwamnati za ta raba gidajen sauro guda miliyan 3.5 wa mutane kyauta a jihar.

Zakari ya fadi haka ne ranar Laraba a garin Dutse.

Ya ce gwamnati ta yi haka ne domin kare mutanen jihar daga kamuwa da zazzabin cizon sauro musamman yanzu da damina ta zo.

” Gwamnati ta horas da wadanda za su raba wa mutane wadannan gidajen sauro sannan tana sa ran cewa kowani gida zai sami akalla gidan sauro biyu a rabon da za a yi.”

A karshe Zakari ya yi kira ga gidajen jaridu da masu fada a ji kan su hada hannu da gwamnati domin wayar da kan mutane kan hanyoyin guje wa kamuwa da cutar.

Share.

game da Author