A yau ne gwamnatin Najeriya ta yi magana a karon farko dangane da bahallatsar Ministar Harkokin Kudade, Kemi Adeosun wadda ta mallakai shaidar sahale mata aikin bautar kasa na NYSC, amma na bogi.
Wakilin PREMIUM TIMES a fadar Shugaban Kasa, ya ritsa Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed, inda ya jefa masa wannan tambayar, kuma ya nemi amsa.
Minista Lai yace ai babu wani abu da zai iya kara cewa, domin Hukumar NYSC ta rigaya ta yi magana.
“Hukumar NYSC ai wani bangare ne na gwamnati, kuma ta yi magana. Don haka babu wani abin da zan iya karawa.” Inji Lai.
Wannan ne karon farko da wani jami’in gwamnatin Muhammadu Buhari ya furta wani abu dangane da harkallar Kemi.
Tabbatattu kuma sahihan shaidun bayanai rubutattu sun tabbatar da cewa Ministar Harkokin Kudi, Kemi Adeosun ba ta yi aikin bautar kasa ba, kuma a lokacin shekarun ta ba su kai na wadda aka dauke wa aikin bautar kasar ba.
Dokar Najeriya ta tanaji hukunci ga wanda duk ya ki zuwa aikin bautar kasa da gangan matsawar dai bai cika shekaru 30 ba.
Akwai daurin shekara uku ko tarar naira dubu biyu, ga wanda ya karya wannan doka, kamar yadda Kemi ta yi.
Akwai kuma daurin shekara uku da doka ta tanadar ga wanda ya kuskura ya buga satifiket na karyar yin bautar kasa.
Takardun karatun Kemi da ke hannun PREMIUM TIMES sun nuna cewa hukumar ta ba ta satifiket na yafe mata zuwa bautar kasa a shekarar 2009, a bisa yawan shekaru.
Discussion about this post